Zab 79:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Suka zubar da jinin jama'arka kamar ruwa,Jini ya yi ta gudu kamar ruwaKo'ina a Urushalima,Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.

4. Sauran al'ummar da take kewaye da mu,Suka maishe mu abin ba'a, suka yi mana dariya,Suka yi mana ba'a.

5. Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji?Har abada ne?Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?

6. Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada,Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!

7. Sun karkashe mutanenmu,Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.

Zab 79