Zab 78:59-62 Littafi Mai Tsarki (HAU)

59. Allah ya yi fushi sa'ad da ya ga haka,Don haka ya rabu da jama'arsa ɗungum.

60. Ya bar alfarwarsa da take a Shilo,Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.

61. Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari,Inda aka ga ikonsa da darajarsa,

62. Ya ji fushi da jama'arsa,Ya bar abokan gābansu su karkashe su.

Zab 78