Zab 75:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo,Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi,Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha,Suka shanye shi ƙaƙaf.

9. Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba,Ko in daina raira yabbai gare shi.

10. Shi zai karya ikon mugaye,Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.

Zab 75