Zab 75:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka!Muna shelar sunanka mai girma,Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!

2. “Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah,“Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.

3. Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace,Zan ƙarfafa harsashin gininta.

Zab 75