Zab 7:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan,Wato idan na yi wa wani laifi,

4. Idan na ci amanar abokina,Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,

5. To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni,Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni,Su bar ni ƙasa, matacce!

6. Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji,Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana!Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi.

Zab 7