14. Sa'ad da Allah Mai Iko DukkaYa warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon,Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.
15. Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?
16. Me ya sa, daga manyan kawunankaKake yi wa dutsen da Allah ya zaɓaYa zauna a kai, duban raini?A nan Ubangiji zai zauna har abada!
17. Daga Sinai da dubban manyan karusansa,Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.