1. Ya Allah, ka ji kukana,Ka ji addu'ata!
2. Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai,Zan yi kira gare ka!Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.
3. Kai ne kāriyata mai ƙarfiDa take kiyaye ni daga maƙiyana.
4. Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina,Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.