2. Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki,Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3. Daga sammai Allah zai amsa mini,Zai kori waɗanda suka tasar mini,Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4. Raina yana tsakiyar zakoki,Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5. Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6. Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,Damuwa ta fi ƙarfina.Sun yi wushefe a kan hanyata,Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.