Zab 51:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yi mini jinƙai, ya Allah,Sabili da madawwamiyar ƙaunarka.Ka shafe zunubaina,Saboda jinƙanka mai girma!

2. Ka wanke muguntata sarai,Ka tsarkake ni daga zunubina!

3. Na gane laifina,Kullum ina sane da zunubina.

4. Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,Na kuwa aikata mugunta a gare ka.Daidai ne shari'ar da ka yi mini,Daidai ne ka hukunta ni.

Zab 51