Zab 5:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ya Sarkina, Allahna,Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.

3. A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji,Da safe za ka ji muryata,Da hantsi zan yi addu'ata,In kuma jira amsa.

4. Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,Ba ka yarda da mugunta a gabanka.

5. Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,Kana ƙin mugaye.

6. Kakan hallakar da duk maƙaryata,Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.

Zab 5