Zab 5:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka kāshe su, ka hukunta su, ya AllahKa watsar da mugayen shirye-shiryensu,Ka kore su daga gabanka sabili da yawan zunubansu,Da kuma tayarwar da suke yi maka.

11. Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki,Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna.Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka,Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.

12. Ka sa wa masu yi maka biyayya albarka, ya Ubangiji,Alherinka yana kāre su kamar gārkuwa.

Zab 5