Zab 48:8-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Mun ji labarin waɗannan al'amura,Yanzu kuwa mun gan suA birnin Allahnmu, Mai Runduna,Zai kiyaye birnin lafiya har abada.

9. A cikin Haikalinka, ya Allah,Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.

10. A ko'ina jama'a suna yabonka,Sunanka ya game duniya duka.Kana mulki da adalci.

Zab 48