1. Ubangiji mai girma ne,Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu,A kan tsattsarkan dutsensa.
2. Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,Mai kyan gani ne na Allah,Birnin babban Sarki.Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!
3. Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,A kagarar birnin.