5. Allah ya hau kan kursiyinsa!Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,Lokacin da Ubangiji yake hawa!
6. Ku raira yabbai ga Allah,Ku raira yabbai ga sarkinmu!
7. Allah sarki ne na duniya duka,Ku yabe shi da waƙoƙi!
8. Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki,Yana mulkin al'ummai,
9. Masu mulkin al'ummai suka tattaruTare da jama'ar Allah na Ibrahim.Allah shi ne garkuwar jarumawa,Yana mulkin duka!