Zab 37:26-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. A koyaushe yakan bayar a sake,Yana ba da rance ga waɗansu,'Ya'yansa kuwa dalilin albarka ne.

27. Ka rabu da mugunta ka aikata nagarta,Za ka kuwa zauna a ƙasar har abada,

28. Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai,Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa,Yana kiyaye su koyaushe,Amma za a kori zuriyar mugaye.

29. Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Su gāje ta har abada.

30. Kalmomin mutumin kirki suna da hikima,Yana faɗar abin da yake daidai.

31. Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.

32. Mugu yakan yi fakon mutumin kirki,Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,

33. Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba,Ko kuwa yă bari a kāshe shiSa'ad da ake masa shari'a.

Zab 37