Zab 36:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa,Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.

2. Domin yana ganin kansa shi wani abu ne,A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba,Ya hukunta zunubinsa.

3. Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi,Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.

4. Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,Halinsa ba shi da kyau,Ba ya ƙin abin da yake mugu.

Zab 36