Zab 21:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki yana murna, ya Ubangiji,Domin ka ba shi ƙarfi,Yana cike da farin ciki,Don ka sa ya ci nasara.

2. Ka biya masa bukatarsa,Ka amsa roƙonsa.

3. Ka zo gare shi da albarka mai yawa,Ka sa kambin zinariya a kansa.

Zab 21