8. Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai,Dukan duniya kuma za ta zama taka.
9. Za ka mallake su da sandan ƙarfe,Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”
10. Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,Ku mai da hankali, ku mahukunta!
11. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro,Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,