Zab 148:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Ubangiji daga sama,Ku da kuke zaune a tuddan sama.

2. Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa,Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!

3. Ku yabe shi, ku rana da wata,Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!

Zab 148