Zab 147:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'an nan yakan ba da umarni,Ƙanƙara kuwa ta narke,Yakan aiko da iska, ruwa kuwa yakan gudu.

19. Yana ba Yakubu saƙonsa,Koyarwarsa da dokokinsa kuma ga Isra'ila.

20. Bai yi wa sauran al'umma wannan ba,Domin ba su san dokokinsa ba.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Zab 147