Zab 145:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka,Ni kuwa zan yi shelar girmanka.

7. Za su ba da labarin girmanka duka,Su kuma raira waƙa a kan alherinka.

8. Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi,Cike da madawwamiyar ƙauna.

9. Shi mai alheri ne ga kowa,Yana juyayin dukan abin da ya halitta.

10. Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka,Jama'arka kuma za su yi maka godiya!

11. Za su yi maganar darajar mulkinka,Su ba da labarin ikonka,

12. Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.

13. Mulkinka, madawwamin mulki ne,Sarki ne kai har abada.

14. Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala,Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.

15. Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi,Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,

Zab 145