Zab 145:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Kowace rana zan yi maka godiya,Zan yabe ka har abada abadin.

3. Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa,Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.

4. Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara,Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.

5. Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka,Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

6. Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka,Ni kuwa zan yi shelar girmanka.

7. Za su ba da labarin girmanka duka,Su kuma raira waƙa a kan alherinka.

8. Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi,Cike da madawwamiyar ƙauna.

Zab 145