Zab 145:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina,Zan yi maka godiya har abada abadin.

2. Kowace rana zan yi maka godiya,Zan yabe ka har abada abadin.

3. Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa,Girmansa ya fi ƙarfin ganewa.

Zab 145