Zab 140:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.

4. Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,Waɗanda suke shirya fāɗuwata.

5. Masu girmankai sun kafa mini tarko,Sun shimfiɗa ragar igiya,Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.

Zab 140