Zab 139:22-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,Na ɗauke su, su abokan gābana ne.

23. Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,Gwada ni, ka gane damuwata.

24. Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.

Zab 139