159. Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
160. Cibiyar dokarka gaskiya ce,Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.
161. Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili,Amma maganarka ce nake girmamawa.
162. In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka,Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.
163. Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu,Amma ina ƙaunar dokarka.
164. A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,Saboda shari'unka masu adalci ne.