Zab 119:142-145 Littafi Mai Tsarki (HAU)

142. Adalcinka zai tabbata har abada,Dokarka gaskiya ce koyaushe.

143. A cike nake da wahala da damuwa,Amma umarnanka suna faranta zuciyata.

144. Koyarwarka masu adalci ne har abada,Ka ba ni ganewa domin in rayu.

145. Ina kira gare ka da zuciya É—aya,Ka amsa mini, ya Ubangiji,Zan yi biyayya da umarnanka!

Zab 119