Zab 119:138-144 Littafi Mai Tsarki (HAU)

138. Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,Daidai ne kuwa.

139. Fushi yana cina kamar wuta,Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.

140. Alkawarinka ba ya tashi!Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!

141. Ni ba kome ba ne, rainanne ne,Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.

142. Adalcinka zai tabbata har abada,Dokarka gaskiya ce koyaushe.

143. A cike nake da wahala da damuwa,Amma umarnanka suna faranta zuciyata.

144. Koyarwarka masu adalci ne har abada,Ka ba ni ganewa domin in rayu.

Zab 119