6. Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki?Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle,Kuna kewayawa kamar tumaki?
7. Ki yi rawar jiki, ya ke duniya,Saboda zuwan Ubangiji,A gaban Allah na Yakubu,
8. Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa,Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai,Masu bulbulo da ruwa.