5. Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.
6. Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,Ba za a taɓa mantawa da shi ba.
7. Ba ya tsoron jin mugun labari,Bangaskiyarsa tana da ƙarfi,Ga Ubangiji yake dogara.