Yush 4:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Duk da haka kada wani ya sa wa mutum laifi,Kada wani kuma ya tsautar.Da ku nake magana, ku firistoci.

5. Za ku yi tuntuɓe da rana,Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare,Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.

6. Mutanena sun lalace saboda jahilci.Tun da yake sun ƙi ilimi,Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina.Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka,Ni ma zan manta da 'ya'yanku.

7. “Yawan ƙaruwar firistoci, yawan ƙaruwar zunubi.Zan sāke darajarsu ta zama kunya.

8. Suna ciyar da kansu da zunubin mutanena,Suna haɗamar ribar muguntarsu.

9. Kamar yadda mutane suke, haka firistocin suke,Zan hukunta su saboda al'amuransu,Zan sāka musu gwargwadon ayyukansu.

Yush 4