Yow 3:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “A wannan lokaci zan mayar waYahuza da Urushalima dawadatarsu.

2. Zan tattara dukan al'ummai,In kai su kwarin Yehoshafat.A can zan yi musu shari'aA kan dukan abin da suka yi wajama'ata.Sun warwatsa Isra'ilawa a sauranƙasashe,Suka rarraba ƙasata.

3. Sun jefa kuri'a a kan mutanena,Sun sayar da yara, mata da maza,zuwa bautaDon su biya karuwai da ruwaninabi.

4. “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.

Yow 3