Yak 3:17-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.

18. Daga irin salama wanda masu sulhuntawa suke shukawa akan girbe adalci.

Yak 3