12. Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.
13. Ina mai hikima da fahimi a cikinku? To, ta kyakkyawan zamansa sai ya nuna aikinsa da halin tawali'u da hikima suke sawa.
14. Amma in kuna da matsanancin kishi da sonkai a zuciyarku, kada ku yi alwashi da haka, kuna saɓa wa gaskiya.
15. Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga Sama ba ce, ta duniya ce, ta son zuciya , ta Shaiɗan kuma.
16. A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.