5. Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!”
6. Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”
7. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8. Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata.
9. Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba.