1. “Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.
2. Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.
3. Za su yi haka ne kuwa domin ba su san Uba ko ni ba.
4. Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.”“Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.
5. Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’