Yah 13:17-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.

18. Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’

19. Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.

Yah 13