11. Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala'ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.
12. Bala'in farko ya wuce, ga kuma bala'i na biyu a nan a tafe.
13. Sa'an nan mala'ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji wata murya daga zankayen nan huɗu na bagadin ƙona turare na zinariya a gaban Allah,
14. tana ce wa mala'ikan nan na shida mai ƙaho, “Ka saki mala'iku huɗun nan da suke a ɗaure a gabar babban kogin nan Yufiretis.”