8. Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu'in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.
9. Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.
10. Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”
11. Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.