12. suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”
13. Sai na ji kowace halittar da take a Sama, da ƙasa, da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da yake cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wanda yake a zaune a kan kursiyin, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!”
14. Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin! Amin!” Dattawan nan kuma suka fāɗi suka yi sujada.