W. Yah 5:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A hannun dama na wanda yake zaune a kursiyin kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai.

2. Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika, yana shela da murya mai ƙarfi cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?”

3. Ba kuwa wani a Sama ko a ƙasa, ko a ƙarƙashin ƙasa, da zai iya buɗe littafin, balle yă duba a cikinsa.

4. Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba a cikinsa ba, ko ɗaya.

5. Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”

6. Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.

7. Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wanda yake a zaune a kan kursiyin.

W. Yah 5