1. “Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.
2. “ ‘Na san ayyukanka, da famarka, da jimirinka, da yadda ba ka iya haƙurce wa mugaye, ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne.
3. Na sani kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
4. Amma ga laifinka, wato, ka yar da ƙaunar da ka yi tun daga farko.