1. Sai ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwar nan, wadda take zaune a bisa ruwa mai yawa,
2. wadda sarakunan duniya suka yi fasikanci da ita, wadda kuma mazaunan duniya suka jarabtu da yin fasikanci da ita.”
3. Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.