19. Sai mala'ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba a cikin babbar mamatsar inabi ta fushin Allah.
20. Aka tattake mamatsar inabin a bayan gari, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.