W. Yah 13:16-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Har wa yau, sai ta sa a yi wa kowa alama a hannun dama, ko a goshi, manya da yara duka, mawadata da matalauta, ɗa da bawa,

17. har ba mai iya saye ko sayarwa sai ko yana da alamar nan, wato, sunan dabbar nan, ko kuwa lambar sunanta.

18. Wannan abu sai a game da hikima. Duk mai basira ya ƙididdige lambar dabbar nan, don lamba ce ta wani mutum, lambar kuwa ɗari shida ce da sittin da shida.

W. Yah 13