1. Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.
2. Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,