7. Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba.Ba rigyawar da za ta nutsar da ita.Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya,Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.
8. Muna da 'yar'uwa ƙunƙuma.Me za mu yi idan wani saurayi ya ce yana sonta?
9. Da a ce ita bango ce, da mun gina mata hasumiyar azurfa.Da a ce ita ƙofa ce, da mun yi mata ƙyaure da itacen al'ul.
10. Ni bango ce, doguwa, mamana tantsai tantsai,Na sami kwarjini wurin ƙaunataccena.