9. Ke mafi kyau cikin mata,Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake.Wane abin sha'awa take gare shi,Har da za mu yi miki alkawari?
10. Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11. Gashin kansa dogaye ne suna zarya,Baƙi wulik kamar jikin shaya.Kansa ya fi zinariya daraja.
12. Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama,Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.