Tit 3:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Amma sa'ad da alherin Allah Mai Cetonmu da ƙaunarsa ga 'yan adam suka bayyana,

5. sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,

6. wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.

7. Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.

Tit 3