Tit 2:13-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,

14. wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.

15. Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗar da su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa yă raina ka.

Tit 2